Yayin da ake ci gaba da gabatar Da Shari'ar waɗanda ake zargin da yunƙurin kifar da gwamnatin Bila Ahmad Tinubu, Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya ce za a saki mutanen da aka kama bisa zargin sa hannunsu a wani yunƙurin shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, idan bincike ya nuna cewa ba su da laifi.
Christopher ya bayyana hakan ne yayin da ya gabatar da wata hira da Channels Television, inda ya ce hukumomin tsaro suna gudanar da bincike domin tabbatar da cewa ba a hukunta mutanen da ba su da hannu a lamarin ba.
Ya ƙara da cewa, waɗanda aka tabbatar da cewa su ne manyan masu ruwa da tsaki a shirin ne kawai za a gurfanar da su gaban kotu, domin a yanke masu hukuncin da ya dace da su.
Ministan ya kuma tabbatar da cewa zargin yunƙurin juyin mulkin na gaskiya ne, yana mai cewa waɗanda ake zargin sun yi niyyar aiwatar da shi. Ya ce DSS da NIA na ci gaba da bincike, yayin da wasu daga cikin waɗanda aka kama tuni aka gurfanar da su a kotu.
An fara samun labarin zargin shirin juyin mulkin ne a shekarar 2025, bayan da aka kama wasu manyan jami’an soji bisa zargin karya dokokin aikin soja. Daga baya gwamnati ta shigar da ƙara kan wasu mutane da ake zargi da hannu a lamarin, da laifukan cin amanar ƙasa, ta’addanci da kuma safarar kuɗaɗen tallafa wa ta’addanci.
Musa ya buƙaci ‘yan Nijeriya su kare dimokuraɗiyya tare da magance matsalolin ƙasar ta hanyoyin dimokuraɗiyyar.