Gwamna Uba Sani Ya Jagoranci Kaddamar da Sabbin Motoci Kirar Peugeot 3008 da 5008 na 2026, Na Kamfanin DPAN

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya halarci taron ƙaddamar da sabbin motocin Peugeot 3008 da Peugeot 5008 na shekarar 2026, mallakin kamfanin Dangote Peugeot Automobile Nigeria Limited (DPAN).

Gwamnan ya bayyana ƙaddamar da motocin a matsayin wata babbar alama ta ci gaban masana'antar ƙera motoci ta Nijeriya, yana mai yabawa DPAN kan jajircewarta wajen ƙirƙire-ƙirƙire da ƙarfafa masana'antu na cikin gida da bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa.

Gwamna Uba Sani ya ce, irin waɗannan abubuwan na ci gaba, suna ƙara taimakawa wajen samar da ayyukan yi ga al'umma, tare da canja fasaha da kuma haɓaka ci gaban masana'antu a ƙasar.

A matsayin goyon baya ga kamfanin, gwamnan ya yi alƙawarin miƙa takardun mallakar filin DPAN, tare da ɗaukar alƙawarin tuntuɓar sauran gwamnoni domin su tallafa tare da sayen motocin kamfanin a faɗin Najeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post