UAE Ta Yi Wa Mawakin Adawar Masar Al-Qaradawi Afuwa Bayan Yanke Masa Hukuncin Shekara 10

 Shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), Sheikh Mohamed bin Zayed Al Nahyan, ya yi wa Abdul Rahman Yusuf al-Qaradawi, wani ɗan adawar gwamnati kuma mawaƙin Masar, afuwa bayan kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 10 a gidan yari.

Abdul Rahman Yusuf al-Qaradawi

Kotun Ƙoli ta Abu Dhabi ta yanke masa hukuncin ne a ranar 27 ga Agusta 2026, tare da ci tarar dirham 200,000, bisa zargin aikata ayyukan da ke neman tayar da hankali da kuma raunana tsaron jama'a.

Al-Qaradawi, wanda ɗan marigayi malamin addinin Musulunci Yusuf al-Qaradawi ne, an kama shi a Lebanon a watan Disamba 2024, kafin daga bisani a mika shi zuwa UAE a watan Janairu 2025. An ce kama shi ya biyo bayan kalaman da ya yi a wani bidiyo na intanet yana sukar hukumomin UAE, Saudiyya da Masar.

Rahotanni sun ce an riga an ɗauki matakan aiwatar da afuwar shugaban UAE, ko da yake ba a bayyana a fili ko an riga an sake shi daga gidan yari ba.

Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da wasu masana na Majalisar Ɗinkin Duniya sun taɓa yin kira da a sake shi, suna cewa an tsare shi ne saboda amfani da haƙƙinsa na faɗar albarkacin baki.

Post a Comment

Previous Post Next Post