Kotun Masar Ta Yanke Wa Mai Gabatar da Shirye-shiryen Talabijin da Wasu 11 Hukuncin Kisa

Wata kotu a Masar ta yanke wa fitacciyar mai gabatar da shirye-shiryen talabijin, Sarah Khalifa, da wasu mutane 11 hukuncin kisa bisa zargin kera da safarar miyagun ƙwayoyi, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito a ranar Asabar.Sarah Khalifa, mai shekara 39, ta fi shahara ne da shirin talabijin ɗinta mai suna “Mission Impossible”, wanda ya fi mayar da hankali kan batutuwan tsaro da laifuka.

Jaridar Al-Ahram, mai alaƙa da gwamnatin Masar, ta ruwaito cewa wata kotu a birnin Alkahira ta yanke wa Khalifa da sauran waɗanda ake tuhuma hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta same su da laifin kafa wata ƙungiyar masu aikata laifuka da ta ƙware wajen samo kayan da ake amfani da su wajen kera miyagun ƙwayoyi da nufin safarar su, tare da mallaka da kuma ɗauke da bindigogi da harsasai ba tare da lasisi ba.

Kotun ta yanke hukuncin ne bayan ta nemi ra’ayin addini daga Babban Mufti na Masar, matakin da dokar ƙasar ta tanada a shari’o’in da za a iya yanke hukuncin kisa.

Sai dai hukuncin kotun na ƙarƙashin ikon ɗaukaka ƙara.

Baya ga aikin gabatar da shirye-shiryen talabijin, Khalifa tana da wani asibitin tiyatar gyaran jiki, sannan tana da kamfanin shirya fina-finai da nishaɗi wanda ya ƙware wajen shirya bukukuwa da sauran taruka.

A cewar jaridar Akhbar Al-Youm, wadda ke ƙarƙashin ikon gwamnatin Masar, an tuhumi waɗanda ake zargin da kera miyagun ƙwayoyi na roba da nufin safarar su, ta hanyar shigo da kayan da ake amfani da su wajen kera ƙwayoyin daga ƙasashen waje.

Jaridar Al-Ahram ta ce jami’an tsaro sun kwace sama da kilogram 750 na miyagun ƙwayoyi da kayan da ake amfani da su wajen kera su. Haka kuma, sun gano wasu gidaje biyu da ake amfani da su a matsayin dakunan gwaje-gwajen kera ƙwayoyin, tare da bindigogi da harsasai marasa lasisi.

Kotun ta kuma yanke wa Khalifa da wasu daga cikin waɗanda ake tuhuma hukuncin ɗaurin shekara biyar a wani shari’a daban da ta shafi sace wani matashi da kuma yi masa duka.

Masar na aiwatar da hukuncin kisa a laifukan da suka haɗa da kisan kai da gangan, ta’addanci, wasu nau’o’in fyade da kuma safarar miyagun ƙwayoyi.

A cewar Egyptian Commission for Rights and Freedoms, kotunan Masar sun yanke hukuncin kisa guda 541 a shekarar 2025.

Post a Comment

Previous Post Next Post