Wakilan Trump za su Gana da Rasha da Ukraine Domin Kawo Karshen yaki

Ana sa ran a yau jakadun shugaba Donald Trump, da suka hada da surukinsa Jared Kushner da kuma Steve Witkoff, za su isa birnin Moscow a wani sabon yunƙuri na kawo ƙarshen yaƙin da ake tsakanin Rasha da Ukraine.

Mista Trump ya bayyana cewa wakilan nasa za su gabatar da sabbin shawarwari na zaman lafiya, sai dai bai yi cikakken bayani kan abin da shawarwarin suka ƙunsa ba.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya ce daga nan wakilan na Amurka za su ziyarci birnin Kyiv a gobe Lahadi, duk da cewa har yanzu Washington ba ta tabbatar da hakan ba. Mista Zelensky ya kuma gabatar da shawarwari na tsagaita wuta na ɗan lokaci a ƙarshen mako.

A gefe guda kuma, jami'an Ukraine sun ce Rasha ta kai hari kan wata cibiyar masana’antu a yankin Dnipropetrovsk cikin dare, inda mutum huɗu suka mutu sannan wasu biyar suka jikkata.

Post a Comment

Previous Post Next Post