Kwamitin musamman na Majalisar Wakilai da ke binciken wata hukuma ta bogi mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) ya ce babu wata shaida da ke nuna cewa Femi Gbajabiamila, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, yana da hannu wajen kafa ko gudanar da hukumar.
Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi, ya bayyana hakan a rahoton farko na kwamitin da aka fitar a Abuja.
Kwamitin ya ce wata wasiƙar da aka yi amfani da ita wajen naɗa Adeniyi Adeyemi a matsayin Darakta-Janar na PFIPC an ƙirƙira ta ne, kuma ba Gbajabiamila ya sanya hannu ko ya bayar da ita ba.
Rahoton ya kuma ce Gbajabiamila ya sanar da hukumomin tsaro bayan samun rahoton zargin damfara da hukumar ke yi, ciki har da ’yansanda, DSS, EFCC da Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro.
Kwamitin ya gano cewa PFIPC ba ta samu sahihin tushe daga wata doka ta Majalisa, umarnin zartarwa ko wani ingantaccen tsarin doka ba. Sai dai an zargi hukumar da amfani da takardun bogi wajen samun wasu damar gwamnati, ciki har da ofishi da kuma wasu abubuwan more rayuwa.
Kwamitin ya kuma bayar da shawarar gudanar da ƙarin bincike kan wasu mu’amalolin kuɗi da ake zargin hukumar ta yi.
Gagdi ya jaddada cewa rahoton da aka fitar na farko ne, kuma bai zama rahoton ƙarshe ko matsayar Majalisar Wakilai ba.
