Miyetti Allah Ta Nemi Tinubu Ya Sa Baki Wajen Sakin Shugabanta

Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore ta shiyyar Arewa ta Tsakiya ta yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da sauran hukumomin gwamnati da su sa baki domin a sake shugabanta na ƙasa, Abdullahi Bello Bodejo, wanda aka sake kama shi bayan an sake shi daga hannun EFCC.

Miyetti Allah

Shugaban kungiyar na Arewa ta Tsakiya, Idris Bebeji, ne ya yi kiran a wani taron manema labarai da aka gudanar a Karu, Jihar Nasarawa.

Bebeji ya ce Bodejo ya shafe kusan watanni huɗu a hannun EFCC bayan da DSS ta kama shi a Jalingo, Jihar Taraba, a lokacin da yake shirin bayyana aniyarsa ta neman kujerar Sanata mai wakiltar Taraba ta Tsakiya.

Ya ce bayan Bodejo ya cika sharuddan sakin da aka gindaya masa kuma aka sake shi, jami’an DSS sun sake kama shi a ranar 28 ga Agusta, 2026.

Kungiyar ta nemi Tinubu, Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, Ministan Shari’a Lateef Fagbemi, shugabannin APC da DSS su duba batun, domin tabbatar da cewa ana mutunta haƙƙin ɗan Adam da bin tsarin doka.

Bebeji ya jaddada cewa kungiyar ba ta neman a fifita Bodejo a kan doka, sai dai ta bukaci a bi tsarin shari’a yadda ya kamata. Ya kuma yi kira ga mambobin kungiyar da al’ummar Fulani makiyaya su kasance cikin nutsuwa tare da bin doka yayin da ake kokarin warware matsalar ta hanyar tattaunawa da tsarin kundin tsarin mulki.

Post a Comment

Previous Post Next Post