Mai Horas da Kungiyar Real Madrid José Mourinho Ya Bayyana Ra'ayinsa Game da Kwallon da Erling Haaland Ya Ci Manchester United Mai Cike da Kalubale

Bayanan José Mourinho game da ƙwallon Erling Haaland mai cike da cece-kuce ya ci ƙungiyra Manchester United:

José Mourinho ya ce: “Na kalli maimaitawar bidiyon (replay), kuma na tabbata, masu alhakin duba ƙwallon sun duba Haaland sannan suka yanke shawarar cewa yatsan ƙafarsa bai shiga offside ba (onside). Shi ke nan. Idan har abin da fasahar ta nuna ke nan, zan iya karɓar hakan.
Amma tambayata a nan ita ce: wane ne ya duba Enzo Fernandez?

Saboda kowa maganar yatsan ƙafar Haaland kawai yake yi, amma me za a ce game da matsayin Enzo Fernández a lokacin harin (build-up)? Shin yana onside? Shin ya yi wani motsi a wasan (interfering)? Ina layin da aka ja masa yake?"

Ya ƙara da cewa: "Sun shafe sama da minti biyar suna duban wannan ƙwallon, saboda haka nake tsammanin za su duba komai da komai, ba kawai ɓangaren da zai taimaka musu wajen bayar da ƙwallon ba. Idan Haaland yana onside da tazarar santimita ɗaya, abin yana da kyau. Ku nuna mana irin wannan zurfin binciken daki-daki a kan Enzo shi ma. Wannan shi ne abin da ya sa shawarar ta su ta zama abin mamaki. 

Mourinho ya ce, da farko alƙalin wasa ya hura offside, amma VAR ta ɗauki lokaci mai tsawo tana duba lamarin, har sai daga ƙarshe suka gano yatsan ƙafar Haaland yana onside, kawai sai dukkan matakin ya sauya.

Mourinho ya ƙarƙare da cewa, " sun kwashe tsawon mintina biyar don gano matsayin yatsan ƙafa, amma a fili yake ba su samu wadatar lokacin bayyana matsayin Enzo. A wasan hamayya na Manchester Derby bai kamata a bar irin waɗannan tambayoyin a rataye ba. Idan har za a rusa matakin alƙalin wasa, ku nuna wa kowa ainihin dalilin da ya sa kuka yi hakan. In ba haka ba, mutane za su sake yin tambaya, mene ne ainihin abin da suke dubawa?”

Post a Comment

Previous Post Next Post