Sarkin Gumel da ke jihar Jigawa, Ahmed Muhammad Sani ya rasu bayan shafe shekara 46 a kan karagar mulki.
Sakataren masarautar, Alhaji Murtala Aliyu ne ya tabbatar da da BBC rasuwar sarkin a yau Alhamis a birnin Alqahira na ƙasar Masar.Sarkin ya shafe tsawo mako shida a asibitin na birnin Alqahira, a cewar sakataren masarautar.
Marigayin ya kasance ɗaya daga cikin sarakuna arewacin Najeriya mafi jimawa a kan gadon sarauta.
A cewar sakataren masarautar marigayin shi ne sarki na 16 a jerin sarakunan masarautar Gumel kuma sarki mafi daɗewa a tarihin masarautar Gumel.
Ya ce nan gaba ne za a mayar da gawarsa zuwa gida domin shirye-shiryen jana’izarsa.
Ya rasu ya bar matan aure uku da ƴaƴa fiye da 30.
Sakataren masarautar Gumel ya bayyana shi da mutum mai haƙuri da son zumunci da ƙaunar al’ummarsa.
An haife shi a 1939 a garin Gumel da ke jihar Jigawa ta yanzu.
A watan Disamban 1980 ne aka naɗa shi sarkin Gumel bayan rasuwar mahaifinsa tsohon sarkin Gumel, Muhammad Sani.