Tinubu Ya Bukaci A Sake Tsara Dokokin Duniya Don Tabbatar Da Adalci, Daidaito Da Wakilcin Kowa

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira da a gaggauta sake fasalin tsarin shugabancin duniya da cibiyoyin hada-hadar kuɗi na ƙasa da ƙasa, yana mai cewa ya kamata tsarin ya kasance mai wakilci, adalci da kuma amsa buƙatun sauye-sauyen tattalin arziƙi da yawan jama’a na duniya.

Shugaban ya bayyana hakan ne a taron shugabannin BRICS na 2026 da ke gudana a New Delhi, India, a cikin jawabin da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya gabatar a madadinsa. Ya ce Najeriya na goyon bayan sake fasalin Majalisar Ɗinkin Duniya, musamman Kwamitin Tsaro, da kuma tsarin hada-hadar kuɗi na duniya domin su dace da yanayin duniya na yanzu.

Tinubu ya kuma buƙaci a mayar da haɗin gwiwar BRICS daga tattaunawa zuwa aiwatarwa, tare da samun sakamakon ci gaba da za a iya aunawa. Ya gayyaci masu zuba jari na ƙasashen waje da su yi amfani da damar zuba jari da ke Najeriya, yana mai bayyana ƙasar a matsayin ƙofar shiga babbar kasuwar Afirka ƙarƙashin yarjejeniyar African Continental Free Trade Area (AfCFTA).

Shugaban ya ce Najeriya na maraba da ƙarin haɗin gwiwa da ƙasashen BRICS a fannonin fasahar zamani, kamar Fasahar (AI), tsarin ayyukan gwamnati na dijital, harkokin fintech, sadarwa, tsaron yanar gizo, fasahar ƙere-ƙere, makamashi, da noma, da kiwon lafiya, da kuma ababen more rayuwa da sarrafa ma'adanai masu muhimmanci. Ya ce Najeriya na son haɗin gwiwar da zai taimaka wajen musayar fasaha, bunƙasa masana'antu, samar da ayyukan yi da kuma gina jarin ɗan'adam.

Tinubu ya jaddada cewa matasan Najeriya na daga cikin manyan kadarorin ƙasar, musamman saboda ƙirƙire-ƙirƙirensu da harkokin kasuwanci. Ya ce shirye-shiryen gwamnati kamar 3MTT, da Project BRIDGE da shirye-shiryen AI na ƙasa na daga cikin ƙoƙarin bunƙasa fasahar zamani da tattalin arziƙin dijital, yana mai cewa ya kamata Afirka ta daina kasancewa a bayan fagen ci gaban duniya, ta koma sahun gaba wajen bunƙasa tattalin arziƙi da ƙirƙire-ƙirƙirensu.

Post a Comment

Previous Post Next Post