Ali Abdollahi, shugaban hafsoshin rundunar sojojin Iran, ya ce ba za a sake barin jiragen ruwan Amurka su shiga Tekun Fasha ba.
Abdollahi ya ce: "ya kamata shugaban Amurka ya fahimci cewa mafarki kawai yake yi idan ya tunanin cewa sojojinsu za su sake shiga Tekun Fasha. Wannan mafarki ne da ba zai yiwu ba.Ya ƙara da cewa: "Ba za mu bari jiragen ruwan sojan Amurka su shiga Tekun Fasha ba a kowane irin yanayi ko kuma a kowane lokaci."
Wannan na zuwa ne bayan kwamandan rundunar ruwa ta IRGC ya bayyana a jiya cewa: "Amurkawa sun ja da baya zuwa kilomita 600 zuwa 700 daga mashigar Hormuz."
A wani ɓangaren kuma, Shugaban Amurka Donald Trump ya zargi Iran da ƙoƙarin tayar da farashin mai gabanin zaɓen tsakiyar wa'adin majalisar dokokin Amurka.
Trump ya yi zargin cewa Iran na yaɗa abin da ya kira "labaran ƙarya" game da fashewar nakiyoyi da hare-hare kan jiragen ruwa a Mashigar Hormuz domin haifar da fargaba a kasuwannin makamashi.