Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci dakarun Najeriya da su ƙara jajircewa wajen kawar da ta’addanci da ’yan tayar da ƙayar baya domin kare tattalin arzikin ƙasa da tabbatar da zaman lafiya.
Tinubu, wanda Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya wakilta, ya yi wannan Kira ne a ranar Asabar yayin bikin yaye sojoji rukunim 72 (Regular Course) Sojin Ƙasa, Ruwa da Sama, na Nigerian Defence Academy (NDA)
Ya gargadi cewa manufar ’yan ta’adda ita ce su tarwatsa ci gaban ƙasa ta hanyar kafa ƙananan dauloli ta hanyar tashin hankali da yaɗa farfaganda.
“Zan yi amfani da wannan dama wajen jawo hankalinku kan illolin ta’addanci da sauran ƙalubalen tsaro a ƙasarmu. Ku tuna cewa burin ’yan ta’adda shi ne su rusa shirye-shiryen ci gabanmu ta hanyar ƙirƙirar dauloli na bogi,” in ji Tinubu.
Shugaban ya jaddada cewa dole ne Rundunar Sojoji ta kasance tsayin daka wajen kare muhimman abubuwan tattalin arziki da ƙimar ƙasa. Ya kuma bukaci sojojin da su kasance masu jajircewa wajen cika burin kare ƙasa, duk da tsananin ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a yau.
Ya yaba wa NDA saboda amfani da sabbin hanyoyin kimiyya da fasaha a horo da binciken soja, yana mai cewa sabon tsarin karatu da hanyoyin horaswa sun dace da bukatun yaƙe-yaƙen zamani.
Tinubu ya taya soj murna, yana mai cewa wannan lokaci ne mafi dacewa da za su nuna jarumtaka tare da bin ƙa’idojin da aka kafa NDA a kai domin kare ƙasarsu.
Jimillar dalibai 472 aka ɗora musu mukaman soja a dandalin, inda Sojin ƙasa ya samu 218, Rundunar Ruwa 135, da Rundunar Sama 119. An kuma karrama dalibai guda shida saboda bajintarsu a fannin ilimi, horon soja da kuma wasu kwasakwasai.