Atlético Madrid Sun Zazzagawa Fararen Balbelu Kwallaye 5-2 A Gasar Laliga

Julian Álvarez Ya Zura Kwallaye Biyu, Griezmann Ya Sanya Ta Biyar.

Wasan Madrid

Atlético Madrid sun yi abin da ba a gani ba a wannan kakar ta La Liga,  sun doke maƙwabtansu Real Madrid da ci 5-2 a wani dabinsu. Wannan nasara ta zo ne bayan Real Madrid ta farke ƙwallon farko kuma ta ƙara a fafatawar, inda Kylian Mbappé da Arda Güler suka zura kwallaye biyu kafin hutun rabin lokaci. Sai dai Atlético sun dawo da ƙarfi sosai bayan hutun rabin lokaci. 

Alexander Sørloth ya daidaita wasa zuwa 2-2 kafin a tsallaka rabi, sannan Julian Álvarez ya ɗauki nauyin jagorantar nasara ta zura kwallaye biyu, ɗaya daga ciki ne ta hanyar penalty. Ƙwallar ƙarshe kuma Antoni Griezmann ne ya tabbatar da cin nasara ga Atlético. 

Nasarar ta nuna raunin tsarin kariya na Real Madrid, inda suka kasa daƙile hare-haren Atlético musamman a sararin samaniya da dabarun kai hari. 

Atlético yanzu za su ci gaba da haɓaka a matsayinsu a gasar cikin gida, yayin da Real ke bukatar nazari da gyara. Kuma ga magoya baya, wannan rana ce da za a tuna wannan dabin inda Atlético suka nuna cewa ba su tsoron Madrid.

Post a Comment

Previous Post Next Post