Da ma masu iya magana na cewa, hannun da ya saba ƙirga riba watarana dole zai ƙirga faɗuwa.
Yau ƙungiyar 'Yan Madara waɗanda suka shahara da Hala Madrid sun kwashi kashinsu a hannun maƙwabtansu Atlantico Madrid.
Ƙungiyar Atlantico Madrid ta lallasa makwabciyar tata da ci biyar da biyu 5:2 a filin wasan Riyadh Air Metropolitano. Inda Normand ya ci 1 Sorloth ya ci 1 Alvarez ya zura ƙwallaye 2 sai kuma ɗan ƙallon Faransa Antonio Griezmann ya zura ƙwallo 1 a mintunan ƙarshe, a Madrid kuwa Kylian Mbappe ne da Arder Gūler suka ci wa 'yan Madarar ƙwallo.
Wannan shi ne karo na farko da ƙungiyar ta yi rashin nasara tun lokacin da sabon mai horar da ƙungiyar Xabi Alonso ya kama aiki.
Har yanzu dai ƙungiyar Real Madrid ita ce ke jagorantar teburin na Laliga da maki 18 yayin da Atlantico Madrid ke ta 4 da maki 12 kafin a kammala wasannin makon.