Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Liverpool ta samu yin rashin nasara na farko tun da aka fara buga kakar wasa na bana 2025/2026.
Ƙungiyar ta Liverpool ta yi rashin nasara ne a hannun Crystal Palace a wasansu na 6 da ya gudana yau Asabar.
Sarr shi ne wanda ya fara zura ƙwallo ta farko a mintuna na 9, sai kuma Liverpool ta cafke wasan a mintuna na 87, cikin nasara Nketiah ya zura ƙwallon da ta ba wa ƙungiyar Crystal Palace nasara a mintunan ƙarshe na 90+7.