A wasan da ƙungiyar Manchester United ta buga yau a gidan Brentford, ƙungiyar ta sake kwasar kashinta a hannun Brentford da ci 3 da 1. A wasannin Premier League wannan shi ne karo na huɗu da ƙungiyar ke samun galaba a kan ƙungiyar ta Jajayen Aljanu a gidansu a jere.
Wannan shi ne wasa na shida (6) da ƙungiyar ta Red Devils ta buga a wannan kakar, inda ta yi nasarar biyu ta yi canjaras a ɗaya ta kuma yi rashin nasara uku a duka wasannin, inda aka zura masu ƙwallaye 11 a wasanni shida kacal.
Yanzu ne su ne na 13 a ƙasan teburin Premier, kafin a kammala buga wasannin makon.
Daga cikin wasanni 33 da uku da sabon mai horas da ƙungiyar Man Utd, Ruben Amorim ya sha duka a wasanni 17.
Alamu dai na nuna ashe ba matsalar Onana ba ce!
Ku sanar da mu matsalar Manchester United a comment section.