Ganduje, Jibrin, Bichi Da Sauran Manyan Jiga-jigan APC Sun Yi Alkawarin Kwace Kano Daga Hannun NNPP Don Tinubu

 


A yayin da babban zaben 2027 ke ƙaratowa, manyan jiga-jigan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano sun sha alwashin tabbatar da nasarar sake zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da ƙwace ragamar mulki daga hannun jam’iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) a jihar da ke Arewa maso Yamma.


Jiga-jigan sun haɗa da tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje; mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, da kuma dan majalisar wakilai, Hon. Abubakar Bichi. Sun bayyana hakan ne bayan wata ganawa ta sirri da suka gudanar a Abuja ranar Alhamis.

Taron ya samu halartar Ministan Jiha na gidaje, Abdullahi Atta; Sanata Kawu Sumaila; tsohon gwamnan Kano, Kabiru Gaya; Sulaiman Bichi; Hon. Mohammed Garba; da wasu ‘yan majalisar jiha da na tarayya. kwamishinoni, da sauran jiga-jigan jam’iyyar.

Ganduje ya bayyana cewa taron ya mayar da hankali ne wajen nazartar nasarorin da suka samu a jam’iyyar a jihar Kano da kuma tabbatar wa Shugaba Tinubu cewa APC a jihar na goyon bayansa.

Post a Comment

Previous Post Next Post