Daga cikin tsare-tsaren bukin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya na shekarar 2025, wanda za a gabatar a Birnin Dutse na Jihar Jigawa a ranakun 31/12/2025 zuwa 01/01/2026. An shirya gasar rubutun gajerun labaran Hausa a kan batun fasahar AI da tsaro domin ta dace da taken taron na bana, wato Marubuta a Ƙarni na 21: Ƙalubalen Tsaro da Tattalin Arziƙi. Gasa ce wadda za ta kasance a buɗe ga dukkan masu sha'awar shiga daga marubuta maza da mata sanannu da sababbi da ma masu sha'awar fara rubutu matuƙar za su kiyaye ƙa'idojin gasar.
MAUDU'IN GASAR
Gudummuwar Fasahar AI ga Tsaro da
Tattalin Arziƙi
MANUFOFIN GASAR
1. Ƙarfafa marubuta su yi nazari kan yadda
fasahar AI (Artificial Intelligence) ke taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da
tsaro da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.
2. Samar da sababbin ra’ayoyi da
mafita na zamani da za su iya taimaka wa al’umma wajen fuskantar ƙalubalen
tsaro da tattalin arziƙi.
3. Gina wata hanya ta tattaunawa
da musayar ra’ayi kan amfanin fasahar zamani a cigaban ƙasa.
4. Ba wa marubuta damar nuna
fasaha da basira da ƙwarewarsu a fannin rubutu da bincike ko ƙirƙira.
5. Haɗa marubuta da masu amfani da fasahar zamani
domin a samu haɗin
gwiwa wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arziƙi.
6. Ƙarin samar da abin karatu mai inganci da
manufa cikin harshen Hausa.
TSARE-TSAREN SHIGA GASAR
1. Za a aiko da samfurin labarin
da za a rubuta cikin kalmomin da ba su gaza 500 ba kuma ba su wuce 999 ba, ta
wannan adireshin; ranarmarubutanhausa2025@gmail.com daga ranar 21/09/2025 zuwa
ranar 21/10/2024.
2. Za a tace a zaɓi 20 cikin samfurin labaran
da aka turo waɗanda
suka fi burgewa a cikin kwanaki goma (21/10/2025 zuwa 31/10/2025).
3. Za a yi bita ta musamman ga
masu waɗannan samfurin
labaran 20 a kan fasahar AI da tsaro da tattalin arziƙi da kuma rubutun gajerun
labarai(musamman saboda sababbin marubuta).
4. Bayan bitar, za a buƙaci
kowannensu ya rubuto cikakken labarinsa wanda bai gaza kalmomi 1000 ba kuma bai
wuce kalmomi 1,500 ba bayan bitar, daga 15/11/2025 zuwa 15/12/2025.
5. Za a bayyana labaran da suka
yi nasara a wajen bukin Ranar Marubutan Hausa ta Duniya 2025.
SHARUƊƊAN
SHIGA GASAR
1. A tabbatar rubutun ya dace da
batutuwan da suka shafi fasahar AI musamman dangane da tsaro da tattalin arziƙi.
2. A tabbatar an yi amfani da
daidaitacciyar Hausa kuma an kiyaye ƙa'idojin rubutun Hausa.Dole ne amfani da
haruffa masu lanƙwasa(ɓ,
ɗ, ƙ, 'y).
3. A tabbatar an aiko da rubutun
a tsarin Microsoft word ko PDF zuwa ga wannan email ɗin; ranarmarubutanhausa2025@gmail.com.
4. A tabbatar ba a taɓa shiga wata gasa da
labarin da za a turo ba, kuma ba a taɓa
bugawa a jarida ko wata kafa ko zaurukan kafafen sadarwa na zamani ba.
5. Mutane biyu za su iya shiga
gasar da labari ɗaya.
Kuma dole ne a aiko da labari cikin lokacin da aka ƙayyade.
6. Kada labarin ya zamto ya ci
zarafi ko tozarta wata al'umma ko ɗaiɗaikun mutane.
7. Ba a yarda a sake ɗaukar duk labarin da aka
shiga da shi gasar a sake shiga wata gasar da shi ba.
8. A sani, hukunci da sakamakon
alƙalan
gasar shi ne na ƙarshe.
KYAUTUTTUKAN DA GASAR ZA TA
SAMAR?
1. Za a bayar da kyaututtuka ga
labarai uku da suka yi zarra a matakin na 1 zuwa na 3.
2. Za a bayar da takardar shaidar
karramawa ga waɗanda
suka shiga gasar daga na 1 zuwa na 15 kuma za a duba yiwuwar buga labaran nasu
cikin littafin da za a ƙaddamar da shi a taron shekara mai zuwa ta 2026.
Mujaheed Abdullahi Kudan, Ph.D.
A madadin Kwamitin Shirya Gasa na
Ranar Marubutan Hausa 2025.

