Mataimakin Shugaban Ƙasa na Najeriya Zai Jagoranci Tawaga Zuwa Taron Majalisar Ɗinkin Duniya Karo Na 80

Ƙarƙashin umarnin Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu, mataimakinsa, Kashim Shettima, zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron shugabannin ƙasashe karo na tamanin (80) na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda zai gudana a birnin New York na ƙasar Amurka.

Kashim Shettima

Taron zai kasance daga ranar 22 zuwa 28 ga Satumba, inda shugabannin ƙasashen duniya za su halarta domin tattaunawa da kuma muhawara kan muhimman batutuwa na duniya.

A cewar mai magana da yawun mataimakin shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yada labarai, Stanley Nwocha, ana sa ran Shettima zai halarci taron tun daga ranar 22 ga Satumba, tare da sauran shugabannin ƙasashe, domin taron bude baki da kuma tattaunawar da za ta gudana daga 22 zuwa 28 ga watan.

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.



Abu-Ubaida Sani

I provide language services such as translation, transcription, proofreading, interpretation, etc in the Hausa language. I also outsource in Pidgin, Yoruba, Igbo, Fulah, and Kanuri. Contact me through email: abuubaidasani5@gmail.com or WhatsApp: +2348133529736

Post a Comment

Previous Post Next Post