Hukumomin Kasar Libya Sun Cika Hannu da Benjamin Ephraim da Ya Sauya Suna Zuwa Abu Hafs Don Gudanar da Aikin Leƙen Asiri A Kasar

Jami'an tsaro a Libya sun kama Benjamin Ephraim da zargin tura bayanan sirri wa Isra-ila. Sunanshi Abu Hafs, da haka aka san shi, ashe asalin sunansa Benjamin Ephraim. Shi memba ne cikin ƙwararrun jami'an sirri na wata ƙungiya mai suna "Firq
Benjamin Ephraim

at al-Musta'rubin", wata ƙungiya ce ta Isra-ila wacce ke da ilimi a kan ƙasashen Larabawa gaba ɗaya; Harshensu, addininsu, ƙungiyoyinsu, ayyukansu da sauransu. Sannan yana aiki kai tsaye da MOSSAD. MOSSAD ƙungiyar jami'an sirrin Isra-ila kenan, kamar CIA.

Ya shiga Libiya ne ta cikin ƙungiyar ISIS, ya yi ta aiki da su har ya zamo imam a cikinsu, sannan ya kafa tashi ISIS ɗin mai ɗauke da mutane 200. Sun yi ƙarfi har suka yi yunƙurin tsallaka iyakar Egypt don tunzira mutane su fito jihadi, daga ƙarshe asirinsa ya tonu aka kama shi, ƙasar Egypt ɗin ta taimaka wajen tona asirinsa wa ƙasar Libya.

Post a Comment

Previous Post Next Post