Gana, wanda ya bayyana haka ga ’yan jarida a babban taron jam’iyyar PDP a jihar Neja, ya ce jam’iyyar ta shirya dawo da Jonathan a 2027.
Ya yi watsi da rikice-rikicen cikin gida na jam’iyyar, inda ya ce taron tattaunawar shawarwari da jigajigan jam’iyyar suka gudanar a Abuja ya magance duk matsalolin.
Amma iƙirarin Gana ya zo ne kwana biyu bayan Jonathan ya gana da Sanata David Mark, shugaban jam’iyyar haɗin guiwa ta African Democratic Congress (ADC), a Abuja.
’Yan makonni da suka gabata, wani daga cikin jigajigan PDP kuma tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce Jonathan shi ne mafi kyawun zaɓi ga jam’iyyar. Haka zalika, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Abba Moro, ya bayyana cewa jam’iyyar ta riga ta nemi Jonathan ya dawo.
Tsarin rabon tikitin jam’iyyar zuwa Kudancin Najeriya wani ɓangare ne na yunƙurin jawo Jonathan da kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party, Peter Obi, wanda shi ma ya yi ganawar sirri da Jonathan ’yan makonni da suka gabata.
Sai dai, ɓangaren jam’iyyar PDP da ke biyayya ga ministan birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya nuna adawa ga dawowar Jonathan, domin sun riga sun sha alwashin goyon bayan tazarcen shugaban kasa Bola Tinubu.
Shugabannin wannan ɓangare sun riga sun amince da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC mai mulki a 2027.
Sai dai, Gana, yayin da yake magana da ’yan jarida a lokacin babban taron PDP a jihar Neja, ya ce: “A 2015, tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan ya ce burinsa bai kai ya zubar da jinin ’yan Najeriya ba.
Bayan shi, wani shugaban ya yi mulki na tsawon shekaru takwas, kuma yanzu wani ya yi shekaru biyu. ’Yan Najeriya sun ga bambanci, kuma bambancin ya fito fili. Yanzu ’yan Najeriya suna roƙon mu mu dawo da abokinmu, tsohon shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan.Ina tabbatar muku cewa Goodluck Ebele Jonathan zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 a matsayin ɗan takarar PDP, kuma za ku zaɓe shi ya dawo shugaban ƙasa.”
Da aka tambaye shi ko rikicin cikin gida na PDP zai iya tasiri wajen nasarar jam’iyyar a 2027, Gana ya ce: “PDP tana da babbar dama a 2027 saboda ita ce jam’iyyar da ta shafi talakawa kai tsaye. Jigajigan jam’iyyar sun gudanar da taron tattaunawa a Abuja kuma sun warware duk matsalolin.”
Tsohon ministan ya yi iƙirarin cewa ’yan Najeriya na son PDP saboda shirye-shiryen ta masu mayar da hankali kan al’umma.
“Shi ya sa suke tunawa da PDP ƙwarai, kuma suna roƙon mu mu dawo,” in ji shi.
Game da halin tattalin arzikin ƙasar, Gana ya ce: “Wannan gwamnati tana da wasu masu tsaron ƙofa marasa kyau da ke hana masu zuba jari daga ƙasashen waje. Wannan shi ne babban matsalarsu. Najeriya ita ce mafi kyawun wuri da za a ninka kuɗin kasuwanci.”