Ma'aikatar ilimin ƙananun makarantun firamare da na sakandire tare da haɗin gwiwar ƙungiyar British Counsil ƙarƙashin jagorancin kwamishina Hajiya Zainab Musawa, ta kammala bayar da horo na kwana huɗu ga malamai 250 da kuma shuwagabannin makarantu 50 a duka faɗin jihar.
A bayanin rufe bayar da horon wanda aka yi shi ranar 26/09/2025 Kwamishinan ilmin ƙananun makarantun firamare da sakandire Hajiya Zainab Musa Musawa ta sake jaddada yabonta ga gwamna Malam Umaru Dikko Raɗɗa Ph.D wanda ya yi tsayuwar daka don ganin an cicciɓa ilimi zuwa gaba a faɗin jihar Katsina, ta kuma miƙa godiya ga ƙungiyar British Counsil wadda ta mara masu baya suka yi haɗin gwiwa aka kammala wannan aiki.