Kotu A China Ta Yanke Wa Tang Renjian Hukuncin Kisa Saboda Cin Hanci

 Kotun ta tabbatar da cewa tsohon jami’in kasar Sin, Tang Renjian, ya karɓi rashawar kuɗi da gidaje masu darajar fiye da dala miliyan 37 lokacin da yake riƙe da muƙamai daban-daban daga shekarar 2007.

Hoton Tang Renjian

A cewar rahoton, Tang Renjian ya yi amfani da matsayinsa na gwamnati wajen karɓar rashawa daga ‘yan kasuwa da wasu kamfanoni domin ba su fifiko da kariya a harkokin kasuwanci. Wannan al’amari ya jawo hankalin hukumomi, inda daga karshe aka gurfanar da shi a gaban kotu.

An bayyana cewa, rikon amana da rashin gaskiya a irin wannan matsayi na gwamnati ya haifar da gagarumin cikas ga shugabanci da amincin jama’a ga gwamnati. Wannan hukunci na kara jaddada irin tsauraran matakan da kasar Sin ke dauka wajen yakar cin hanci da rashawa.

Hukumar yaki da rashawa ta kasar ta ce wannan shari’ar na cikin jerin shari’o’in da ake gudanarwa a ci gaba da kokarin tsaftace gwamnati da tabbatar da gaskiya a shugabanci, domin karfafa amincewar jama’a da kuma inganta tsari a cikin kasar.

Post a Comment

Previous Post Next Post