Malala Yousafzai Ta Sake Kawo Ziyara Nijeriya A Karo Na Biyu

 WACE CE MALALA Yousafzai?

Malala Yousafzai, wata 'yar Pakistan ce mai fafutukar kare ilimin mata kuma wacce ta sami kyautar Nobel ta zaman lafiya.

· SHEKARU: An haifi Malala

Malala Yousafzai

a shekarar 1997 a Mingora, Pakistan.

· FAFUTUKA: Tun tana yarinya, ta fara fafutukar neman ilimin mata a yankin Swat na Pakistan, inda 'yan Taliban suka hana mata karatu.

· HARI: A shekarar 2012, wani dan Taliban ya harbe ta a kai don ramuwar gayya saboda fafutukar da take yi. Ta sami raunuka masu tsanani amma ta tsira.

· HARI: A shekarar 2014, ta zama mace mafi karancin shekaru (yaro mafi karancin shekaru) da ta ta sami kyautar Nobel, ta raba ta tare da Kailash Satyarthi na Indiya, saboda fafutukar neman ilimin yara a duniya.

· AYYUKA:

  · Ta kafa Malala Fund don tallafa wa ilimin yara mata.

  · Ta rubuta littafin tarihin rayuwarta mai suna "I Am Malala".

  · Ta ci gaba da zama murya ta duniya don ilimi da 'yancin mata.

ZIYARAR MALALA TA FARKO

Malala ta kai ziyara a Yerwa Government Girls School a Maiduguri a shekarar 2017 a wani ɓangare na aikin UNICEF don mayar da yara zuwa makaranta a yankin arewa maso gabas. 

ZIYARAR MALALA TA BIYU

Zuwa yanzu, Malala tana ziyartar Najeriya tun daga ranar 27 ga Satumbar nan har zuwa yau 28/ 09/2025. Ta zo ne tare da Mahaifinta, Ziauddin Yousafzai, da sauran wasu jami'an  zartaswa na Malala Fund, kamar Lena Alfi, duka suna tare da ita.

Manufar ziyarar Malala a Nijeriya ita ce, don inganta muhimman manufofin da suka shafi ilimin 'yan mata a Najeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post