Sanata Kabiru Marafa ya jajanta wa al'ummar ƴandoto da ke ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara. Bisa iftila'in da ya auku na kashe masallata 5 da kuma jikkata wasu, tare da yin garkuwa da wasu.
Sanatan wanda shugaban tafiyar siyar gidan Marafa Alhaji Abubakar Usman Gora ya wakilta. Ya nuna damuwarsa game da faruwar al'amarin, ya yi addu'ar Allah ya gafarta wa waɗanda suka rasu, Ya kuma yi wa waɗanda aka yi garkuwa da su mafita.
Baya ga wannan tawagar sanatan ta ƙara kai ziyarar jajantawa a yankin Mada da ke ƙaramar hukumar Gusau ta jihar Zamfara tare da bayar da tallafi ga mutanen ƙauyukan Dattawa, Zaman zamani, Gidan Iro da Ƙyanƙyashe.
Tawagar ta samu tarbon wakilin Uban ƙasar Mada malam Hamza Wamban Mada. Ya yi godiya a madadin Uban ƙasar. .