A cikin hutun da aka yi ne na kakar wasannin 2024-2025 kafin a dawo buga wasannin Leagues, Diego Jota ɗan ƙwallon Liverpool na ƙasar Portugal ya haɗu da haɗarin mota shi da ƙaninsa wanda hakan ya zama sanadiyyar ajalinsu su duka biyun. Kuma su kaɗai ne mahaifiyarsu ta haifa a duniya.
Jota ya rasu ne a makon da aka ɗaura masa aure da matarsa wadda suke da 'ya'ya uku a tsakaninsu kamar yadda za ku gani a hoton da ke ƙasa.