An saka Naira ta Najeriya a matsayin kuɗi na tara mafi rauni a nahiyar Afirka, bisa rahoton Forbes Currency Calculator na watan Satumba, 2025. Wannan ya nuna ci gaba da matsin tattalin arziki duk da alamun sauƙin hauhawar farashi da aka fara gani a baya-bayan nan.
Forbes currency calculator na amfani da bayanan kasuwannin musayar kuɗi na duniya a zahiri ta hanyar Open Exchange Rates API, wanda ke sabuntawa kowane minti biyar domin nuna darajar kuɗi da ake kasuwanci da shi a ainihi. Tsarin yana bibiyar yanayin kasuwa, da halin tattalin arzikin ƙasa ke shafar karfin ko raunin kuɗin kowace ƙasa.
Mafi Raunin Kuɗaɗe a Afirka (Satumba, 2025)
-
Dobra na São Tomé & Príncipe – 22,282 a kan $1
-
Leone na Saliyo – 20,970
Franc na Guinea – 8,680
Shilling na Uganda – 3,503
Franc na Burundi – 2,968
Franc na Kongo – 2,811
Shilling na Tanzaniya – 2,465
Kwacha na Malawi – 1,737
Naira ta Najeriya – ₦1,490 a kan $1
Franc na Ruwanda – 1,448
Mafi Ƙarfi a Afirka
Dinar na Libiya – 5.40
Dinar na Tunisiya – 2.90 a kan $1
-
Dirham na Moroko – 9.91
-
Cedi na Ghana – 12.31
-
Pula na Botswana – 14.15
Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta tabbatar da cewa ƙasashen Afirka sun kai 54 a halin yanzu.
Hauhawar Farashi Ya Fara Sauƙaƙa a Najeriya
Duk da rauninta, Najeriya ta samu ɗan sauƙi a bangaren hauhawar farashi. Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta bayyana cewa hauhawar farashi ya sauka daga 24.5% a Janairu zuwa 20.12% a Agusta 2025, wanda ya ragu wata biyar a jere.
Masana sun danganta wannan sauƙin da samun kwanciyar hankali a shigar kuɗaɗen musaya daga fitar da mai da kuɗaɗen ’yan ƙasa waje, ingantaccen amfanin gona, da kuma tsauraran manufofin kudi daga Babban Bankin Najeriya (CBN), wanda ya riƙe farashin lamuni (benchmark rate) a 27.5%.
Kungiyar Independent Media and Policy Initiative (IMPI) ta tabbatar da wannan sauƙin hauhawar farashi. Shugabanta, Dr. Omoniyi Akinsiju, ya bayyana cewa:
“Najeriya ta samu wani abin da ba kasafai ake gani ba a 2025, inda hauhawar farashi ya sauka daga 24.5% a Janairu zuwa 20.12% a Agusta wannan shi ne mafi saurin sauƙi a tsawon rabin shekara cikin fiye da shekaru goma.”
Game da makomar tattalin arziki, IMPI ta yi hasashen cewa hauhawar farashi zai ci gaba da raguwa:
Muna hasashen cewa zai iya sauka zuwa 17% kafin ƙarshen Disamba 2025, wanda hakan ke nuna ci gaba da sauƙi da kuma rage matsin lamba ga ’yan kasa,” in ji Dr. Akinsiju.
Masu nazarin tattalin arziki sun ja hankalin cewa matsayi na Naira a jerin kuɗaɗen da suka fi rauni a Afirka ya nuna muhimmancin sake fasalin manufofin musayar kuɗi, ƙarfafa samarwa a cikin gida, da haɓaka asusun ajiya na waje domin dawo da cikakken amincewa da Naira a nan gaba.
-