Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Manchester United, ba ta taɓa jera wasanni biyu ta yi nasarar dukkansu ba a gasar cin kofin Premier League na Ingila tun lokacin da sabon mai horas da ƙungiyar ya kama aiki.
Ruben Amorim ɗan asalin ƙasar Portugal shi ne sabon mai horas da ƙungiyar ta Manchester United wanda ya kama aiki a gab da ƙarshen kakar wasan 2024-2025.
Amorim ya dawo Manchester ne daga ƙungiyar Sporting Lisbon ta Portugal, waɗanda a lokacinsa suke kan teburin gasar ƙasar, amma dai har yanzu abubuwa ba su saitu wa Amorim a Manchester ba, a kakar wasan da ta ƙare, ya ƙare a ƙasan teburi, a yanzu kuma yana na 14 kafin a kammala wasan wannan makon.