Kamar yadda jaridar Katsina Times ta ruwaito, injiniya Magaji Abdullahi Yankara da Injiniya Lukman Rabiu Faskari, matasa ne ‘yan asalin Jihar Katsina, sun ƙera motoci masu amfani da wutar lantarki na gida tare da neman goyon bayan gwamnati domin faɗaɗa wannan aiki na fasaha, yin hakan zai taimaka wa matasan sosai wajen kawo cigaba ga al'ummar jihar Katsina da ma Nijeriya baki ɗaya.
Injiniyoyin, tare da haɗin gwiwar ɗaliban wata makarantar sakandare a Sokoto, sun ƙera motoci masu ɗaukar fasinja daga mutum shida zuwa goma sha biyu. Wannan nasara ta jawo hankalin kafafen yaɗa labarai na cikin gida da na ƙasashen waje, tare da samun yabo daga Hukumar Ƙera Motoci ta Ƙasa (NADDC).
A halin yanzu, matasan suna aiki a Sashen Bincike, Ƙirƙire-kirkire da Cigaba na Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sokoto. Sun bayyana cewa burinsu shi ne su isar da wannan ilimi ga matasan Katsina ta hanyar shigar da darussan fasahar motoci masu lantarki cikin manhajar makarantu. Sun riga sun tsara kundin karatu ga ɗaliban makarantun sakandire tun daga aji ɗaya har zuwa aji uku tare da shirin horas da malamai da za su koyar da ɗalibai.
Haka kuma, sun nuna sha'awar komawa jiharsu ta Katsina domin samar da sashin koyar da fasahar motoci masu lantarki a Cibiyar koyar sana'o'in hannu ta Matasan Katsina wato Katsina Youths Crafts Village (KYCV), domin mayar da jihar cibiyar kirkirar motocin lantarki a Najeriya.
Injiniyoyin sun jaddada cewa suna da ƙwarewar ƙera kowace irin mota ta lantarki, tare da fatan samun haɗin kai da Gwamnatin Katsina wajen inganta fasaha da samar da ayyukan yi ga matasa.
Ƙarfafa guiwa ga matasa a irin wannan fanni na kimiyya da fasa lamari ne da ke kawo cigaba sosai ga al'umma. Ta nan ne matasa ke samun ayyukan yi, su taimaki kansu har ma su taimaki wasu.
