Shekaru kaɗan da suka gabata, lokacin yankin Arewa na zaune lafiya. Hausawa da Fulani na zaman taimakon juna. Babu faɗa ko tsangwama a tsakani, an bar tarihin abubuwa masu daɗi musamman lokacin damina, wato lokacin da Hausawa ke kutsawa cikin jeji domin gudanar da ayyukan gona. Amma yanzu lamarin sam na neman canza salo, ko kuma a ce ma ya canza salo. Daga cikin ababen da za a iya tunawa a lokacin da ake zaune lafiya akwai damina. Haka kuma da lamarin ya canza salo, damina na ɗaya daga cikin abun da za a iya tunawa. Ga yadda lamarin yake a cikin labari:
"Da idan aka tafka ruwan sama, idan gari ya waye sai a nufi jeji. A Yi shuka, bayan wani ɗan lokaci ka ga yabanya ta yi kore shar. Ga kukan tsuntsaye da na ƙwari, ga kuma iska mai daɗi na kaɗawa, a yi ta sha'ani cikin jin daɗi, ba tare da wata fargaba ba.
Kaico! Yanzu kuwa babu abunda ake fama da shi idan damina ta sauka sai ƙarar harbe-harbe musamman a karkara. Ga kuma yin garguwa da mutane. Kullum sai an zubar da jini, kullum sai an ɗebo gawarwaki. Idan aka shiga jeji fargaba ce cike da zukatan mutane. Da an ji motsi kaɗan sai a jefar da fatanyu, a yi ta gudun tsira da rayuwa."
