An hango faifan bidiyon shugaban 'yan Ƙur'ani zalla Malam Yahaya Masussuka yana karanta littafin Hadisi mai suna Shama'il Muhammadi domin kafa hujja.
A baya dai mun san kiran Masussuka ya fi shahara a kan cewa shi fa bai yarda da Hadisi ba kuma ba su aiki da kowane irin Hadisi, duk wani hani ko umarni na addini in dai ba a Ƙur'ani ya zo ba, to su bai shafe su ba. Amma sai ga shi an hango shi yana kafa hujja da Hadisi.
Abin tambaya, yanzu Yahaya Masussuka ya sauka daga koyarwar Ƙur'ani zalla ya koma aiki da Hadisai ne? Ko kuwa iya wannan mas'alar ce kawai ta sa zai yarda da Hadisi a karon farko?
Yadda aka ji yana karanta littafin Shama'ilil Muhammadi sai ka rantse da Allah ba a lokacin ya fara karanta shi ba, domin tun daga gida ya sanya shaidar inda yake son karantawa, ashe da ma suna karanta hadisai aiki ne da shi ba su yi.
Wannan yake tabbatar da lallai a kiraye-kirayen Yahaya Masussuka akwai lauje cikin naɗi haɗi da ɗora mabiyansa akan keken ɓera.
Allah ya ganar da mu gaskiya ya ba mu ikon bin ta.