Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, a ranar Alhamis ya ziyarci garin Oke-Ode da ke ƙaramar hukumar Ifelodun ta jihar, domin jajanta wa al’umma da iyalan da suka rasa ‘yan uwansu a sakamakon hare-haren ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane.
Haka kuma ya aika da saƙon ta’aziyya da jituwa ga dukkan al’ummomin da abin ya shafa – daga Ifelodun zuwa Irepodun, Isin, Ekiti, Edu, da Patigi.
“Mun zo ne domin jajanta wa al’umma bisa hare-haren da aka yi musu. Haka kuma domin mu yaba wa jami’an tsaro, masu gadin daji, da vigilante bisa kokarinsu na mayar da martani da kuma dawo da zaman lafiya ga al’umma,” In ji shi
“Lamarin ya kasance kalubale ƙwarai. Amma duk abin da ya dace ana shiryawa domin rage tasirinsa, tare da tabbatar da kawo ƙarshen irin wannan faruwa,” ya ƙara da cewa.
Gwamnan ya samu rakiya daga kwamishinan ‘yan sanda, Adekimi Ojo; daraktan DSS na jiha; kwamandan NSCDC na jiha, Dr. Umar Mohammed; babban mataimaki na musamman kan harkokin tsaro, Muyideen Aliyu; da kuma shugaban ƙaramar hukumar Ifelodun, Hon. Femi Yusuf.
Gwamnan ya karɓi bayanai daga jami’an tsaro da wasu shugabannin al’umma na Oke-Ode da makwabciyarta Igbaja, ciki har da shugaban ƙasa na ƙungiyar cigaban Oke-Ode, Alhaji Abdulganiyu Ajala, Elder Oyin Zubair, da jagoran matasa.
Tun da farko, gwamnan ya fitar da sanarwa na jajanta wa al’ummomin da abin ya shafa, inda ya ce dole a ƙara ƙoƙari domin kare rayuka da dukiyoyin jama'a