Takardar Trump Ta Ce Amurka Na Cikin “Yakin Da Ba Na Kasa Ba” Da Kungiyoyin Miyagun Kwayoyi

 Gwamnatin Trump Ta Ce Ƙungiyoyin Dillancin Ƙwaya ‘Yan Yaƙi Ne Ba Bisa Ƙa’ida Ba, Don Haka Ana Iya Kai Musu Hari.

Yaƙi

Washington, D.C., Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da Majalisar Dokoki cewa Amurka tana cikin wani irin “yaƙin da ba na ƙasa ba” (non-international armed conflict) da kungiyoyin dillancin miyagun ƙwaya, inda ya bayyana su a matsayin ‘yan yaƙi ba bisa ƙa’ida ba.

Wannan sanarwar, wadda jaridu a Amurka suka samu kwafinta, ta biyo bayan hare-haren soji da aka kai kan jiragen ruwa da ake zarginsu da  safarar ƙwayoyi a yankin Caribbean, lamarin da ya jawo mutuwar mutane da dama. Gwamnatin Trump ta bayar da hujjar cewa ayyukan waɗannan kungiyoyi sun wuce kan safarar ƙwaya kawai, suna zama tamkar hari ga tsaron Amurka da ‘yan ƙasarta.

Martanin Masana da ‘Yan Siyasa

Matakin ya jawo cece-kuce a fagen doka da siyasa. Masu suka sun ce Trump ba shi da ikon ya ayyana irin wannan yaƙi ba tare da amincewar Majalisa ba, kuma hare-haren na iya sabawa doka ta cikin gida da ƙa’idar ƙasa da ƙasa kan amfani da ƙarfin soja. Wasu ‘yan majalisa sun gargadi cewa hakan na iya zama mummunan misali na cin gashin kai daga bangaren shugaban ƙasa.

Takardar ba ta fayyace sunayen ƙungiyoyin da ake kaiwa hari ba, duk da cewa gwamnatin Trump ta dade tana zargin wasu ƙungiyoyin dillanci daga Latin America, musamman na Venezuela.

Post a Comment

Previous Post Next Post