Abubuwan Da Ke Jawo Ciwon Koda

Ka taɓa ganin mutum ya yi ƙuruciya lafiya, amma daga baya sai koda ta lalace har aka fara yin dialysis? Yawanci abin ba yana faruwa ne kwatsam ba – abubuwan da yake yi a kullum ne suke kashe masa ƙoda a hankali.

Hoton Yanayin Koda

. Ga Kaɗan Daga Cikin Abubuwan Da Ke Jawo Ciwon Ƙoda Kamar Yadda Likitoci Suka Bayyana

1. Yawan gishiri – Gishiri na ƙara hawan jini, yana sa ƙoda ta yi aiki fiye da ƙima har ta gaji.

2. Rashin shan ruwa – Idan ba ka shan ruwa sosai, gubobi na taruwa a jiki, ƙoda ta wahala wajen fitar da su har ta gaji.

3. Yawan shan maganin ciwo kamar– Paracetamol, ibuprofen, diclofenac idan aka yi amfani da su ba tare da shawara ba, suna haddasa cutar da ƙoda.

4. Shan giya da taba, dukansu suna lalata jijiyoyin ƙoda.

5. Ciwon sukari da hawan jini da ba a kulawa, Su ne manyan masu lalata ƙoda a hankali.

6. Rashin motsa jiki da ƙiba, Suna ƙara hatsarin kamuwa da cututtukan da ke lalata ƙoda.

7. Shan guba ko sinadarai masu haɗari – Magungunan gargajiya marasa tabbataccen inganci na  ɗauke da sinadarai masu kashe ƙoda.

Kula da lafiya, wani abu ne mai matuƙar muhimmanci ga ɗan'Adam, saboda haka, yana da kyau a kula sosai. Lafiya ita ce babban jarin ɗan'Adam, domin da ita ne ake tunƙaho wajen gudanar da harkokin rayuwa na yau da kullum.

Post a Comment

Previous Post Next Post