Abinda Ya Faru Tsakanin Tai Solarin da Janar Ibrahim Badamasi Babangida

Shekaru da dama, TAI SOLARIN ya zama matsala ga gwamnatin IBB, saboda  tsananin sukar IBB ɗin da yake. Solarin ya na iƙirarin shi mai son talakawa ne. Ya kira gwamnatin Babbangida da cewa ta gaza ta wajen biyan muradun talakawan Najeriya.

Solarin Tai

Watarana, bayan Solarin ya soki gwamnatin IBB a kafafen yaɗa labarai bisa wasu manufofinta, sai IBB ya gayyaci Tai Solarin domin su tattaunawa. IBB ya tambaye shi ko me zai iya yi domin inganta rayuwar talakawa?. Tai Solarin ys yi murna da wannan tambayar. Cikin sauri ya ce a ba da lamuni mai sauƙi ga ɗaukacin talakawan Najeriya don su samu damar fara kasuwanci da inganta ƙananan sana’o’i ta yadda talakawa za su ci gaba da amfana, kuma su riƙa mayar da rancen har sai abin ya kai ga kowa.

IBB ya tafa wa Tai, ya kuma roƙe shi da ya jajirce wajen ganin shirin ya gudana ba tare da wata matsala ba. Tai Solarin ya amince. Nan take gwamnatin IBB ta kafa Bankin Jama’a (People's Bank) ta hanyar dokar soja (Decree), mai lamba 22 na shekarar 1990. Kuma aka zuba maƙudan kuɗaɗe a ciki tare da ba Dr. Tai Solarin shugabancin Bankin. Nan da nan bankin ya fara ba wa talakawa rancen kuɗi don su fara ko faɗaɗa sana’arsu. Daga nan Tai Solarin ya daina sukar gwamnatin IBB.

A lokacin baya, ana fara karɓar lamuni ne daga N50 zuwa N5,000, ba tare da an biya ruwa ba. Amma abin takaici shi ne, bayan bayar da lamunin ga talakawa na wani dogon lokaci, talakawan sai suka ƙi mayar da kuɗin, kuma babu wanda ya ga cigaban kasuwancin da sana"oi a ƙasar domin kuwa talakawa sun bi ta kan kuɗin, sun kashe sun yi bushasha a banza ga shi kuma ba su biya ba. 

Tai Solarin ya shiga cikin damuwa, sai zufa yake faman yi duk da yana cikin na'urar sanyaya office (AC), "wata babbar matsala ita ce" yunƙurin ƙwato bashin yaci tura. Bankin Jama'a (People's Bank) ya rushe. Tai Solarin ya shiga gudu da ɓuya.

A ƙarshe da kansa ya je wurin IBB, amma IBB bai nuna ya fushi ba, sai ma kawai ya ce "Tai ka ga abin da muke fuskanta a gwamnati? Magana ta na da sauƙi da arha, amma yallaɓai dubi bankinka. Wannan ƙaramin banki ne kawai, amma ka kasa sarrafa shi, ka yi tunanin bankuna nawa muke da su, ka yi tunanin mulkin ƙasa baki ɗaya yallaɓai? Idan mutane suka zarge ka da rugujewar bankin da ka nema a kafa kuma ka jagoranta yaya za ka ji? ba za ka damu ba? Kaje gida ka huta lallai ka sha wahala da yawa….Na gode da hidimar da ka yi wa al’umma...”

Amma kafin ya bar Dodan Barracksai, Sai IBB  ya bai wa shugaban Soja na lokacin umarnin a dawo da shi. Tai Solarin ya fara zufa ya na makyarkyata cikin kaɗuwa da tsoro, amma duk da haka ya yi ƙoƙari ya natsu. yana komawa IBB ya tambaye shi, "Shin kana son zama ministan ilimi ko kuɗi?" Abinda da kawai nake bukata daga gare ka shi ne kace eh ko a'a.

Sai Tai Solarin ya amsa da sauri. "Mai girma shugaban ƙasa, ba ka ce in koma gida in huta ba?, ka bar ni kawai na yi tafiya ta." Da wannan ne Tai Solarin ya bar gaban shugaban ƙasa. Daga nan  ba su sake haɗuwa ba, kuma Tai Solarin bai sake sukar IBB ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post