Afghanistan Da Pakistan Sun Yi Ikirarin Cewa Sun Yi Asara A Faɗa Tsakaninsu

Taliban

Rahotanni daga yankin iyakar Pakistan da Afghanistan sun bayyana cewa dakarun Taliban da na Pakistan sun yi artabu mai tsanani, wanda ya jawo asarar rayuka da lalacewar kayan yaƙi.

Kowane ɓangare ya ce ya yi nasara wajen dakile hare-haren ɗayan, inda Taliban ta ce ta kare yankinta daga farmakin Pakistan, yayin da hukumomin Pakistan suka tabbatar da cewa sun halaka ‘yan bindiga masu tsattsauran ra’ayi daga ɓangaren Afghanistan.

Wannan sabon rikici na zuwa ne yayin da dangantakar ƙasashen biyu ke ƙara yin tsami, musamman kan batun tsaron iyaka da kuma ƙungiyoyin da ke kai hare-hare daga ɓangaren ɗaya zuwa ɗaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post