Ciwon ƙoda na nufin wani ciwo ko damuwa da ke tasowa a cikin ƙodar mutum.Ciwon na iya zama mai zafi sosai ko akasin haka, kuma lallai ciwon ƙoda yana buƙatar kulawa da sauri. Yawanci ciwon koda yana faruwa ne saboda wasu dalilai kamar haka: 1- Duwatsu a cikin ƙoda (Kidney stones): Waɗannan sukan haifar da ciwo mai tsanani a bayan mutum ko ƙashin ƙugu. 2- Sannan akwai abinda ake cewa (Kidney infection): Yana haifar da zafi, zazzabi, da kuma ciwon baya. 3- Sai kuma (Kidney cysts): Ƙwayoyin ruwa da za su iya haifar da ciwo idan suka girma sosai. 4- Raunin ƙoda (Kidney injury): Kamar bayan an buge mutum a wani yanki na ƙoda.
. Ƙarin Abubuwan Da Ke Haifar Da Ciwon Koda
1. Yawan gishiri – Gishiri na ƙara hawan jini, yana sa ƙoda ta yi aiki fiye da ƙima har ta gaji.
2. Rashin shan ruwa – Idan ba ka shan ruwa isasshe, gubobi na taruwa a jiki, ƙoda ta wahala wajen fitar da su har ta gaji.
3. Yawan shan maganin ciwo – Paracetamol, ibuprofen, diclofenac idan aka yi amfani da su ba tare da shawara ba suna cutar da ƙoda.
4. Shan giya da taba dukansu suna lalata jijiyoyin ƙoda.
5. Ciwon sukari da hawan jini da ba a kulawa Su ne manyan masu lalata ƙoda a hankali.
6. Rashin motsa jiki da ƙiba Suna ƙara hatsarin kamuwa da cututtukan da ke lalata ƙoda.
7. Shan guba ko sinadarai masu haɗari – Magungunan gargajiya marasa tabbataccen inganci na ɗauke da sinadarai masu kashe ƙoda.
.Muhimman Shawarori
Dole ne a tafi wajen likita a kan lokaci. Ciwon ƙoda na iya zama mai tsanani kuma yana buƙatar bincike na likita. Likita zai yi gwaje-gwaje da na'urar duba cikin jiki (ultrasound) ko kuma gwajin jini da fitsari don gano dalilin da yake haifar da ciwon· A Sha ruwa da yawa· A Sha magungunan hana ciwo (kamar Paracetamol) amma kada a sha magungunan da suka haɗa da ibuprofen (kamar Brufen) ba tare da izinin likita ba domin suna iya cutar da ƙoda idan suna da matsala· Nemi taimakon likita cikin gaggawa.
