AFIT Ta Gargadi Sabbin Dalibai Kan Shaye-Shaye Da Laifukan Intanet Kaduna – Oktoba 31, 2025:

Kwamandan Jami’ar Fasaha ta Sojin Sama (AFIT), Kaduna, Air Vice Marshal Sani Rabe, ya gargaɗi sabbin ɗaliban makarantar da su nisanci shaye-shaye, ƙungiyoyin asiri, da laifukan intanet, yana mai cewa makarantar ba za ta lamunci duk wani nau’in rashin ladabi ba.

Rabe, wanda ke barin muƙaminsa a mako mai zuwa, ya bayyana hakan ne a bikin rantsar da sabbin ɗalibai 1,524 na shekarar karatu ta 2025/2026, da aka gudanar a Kaduna a ranar Juma’a.

Ya ce AFIT tana gudanar da gwaje-gwajen jini lokaci zuwa lokaci domin gano masu amfani da miyagun ƙwayoyi, inda aka kore dalibai 20 cikin shekaru biyu da suka gabata. Ya ƙara da cewa wasu ma’aikata ma sun rasa aikinsu saboda irin wannan laifi.

Kwamandan, wanda Mataimakinsa AVM Albert Bot ya wakilta, ya ce AFIT na aiki tare da EFCC wajen hana da kuma gano masu aikata laifukan intanet a cikin makaranta.

Haka kuma, ya tunatar da sabbin ɗalibai su zama masu ladabi, bin doka da kuma nisantar duk wata ɗabi’a da za ta ɓata sunan makaranta ko iyayensu.

A nasa jawabin, Baƙon Girmamawa, AVM Adebayo Kehinde, ya bayyana AFIT a matsayin muhimmiyar cibiya da ke tallafa wa rundunar sojin sama da kuma ci gaban fasahar Najeriya. Ya buƙaci daliban su mayar da hankali wajen karatu da bin dokokin makarantar.

Post a Comment

Previous Post Next Post