KOTU TA TSIGE DAN MAJALISAR TARAYYA DAGA ZAMFARA KAN SAUYA SHEKA ZUWA JAM’IYYAR APC

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tsige dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum ta jihar Zamfara, Abubakar Gummi, bisa sauya shekarsa daga PDP zuwa APC.

Alkalin kotun, Justice Obiora Egwuatu, wanda ya yanke hukunci a ranar Alhamis, ya bayyana sauya shekar a matsayin ba bisa doka ba, tare da umartar Gummi da ya bar kujerarsa nan take.

A cikin hukuncinsa, mai shari’ar ya kuma hanawa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, daga ci gaba da amincewa da Gummi a matsayin dan majalisa. Haka kuma, ya umurci INEC da ta gudanar da sabon zabe a mazabar cikin kwanaki 30.

Justice Egwuatu ya yi Allah wadai da yawaitar sauya sheka a siyasar Najeriya, yana mai cewa hakan yana tauye dimokuradiyya da kuma cin amanar masu zabe.

’Yan siyasa su dinga mutunta ta ba su tikiti. Ba doka ba ce, kuma ba daidai ba ne mutum ya sauya sheka ba tare da mika kujerar da aka ba shi bisa wannan jam’iyya ba,” in ji shi.

Ya kara da cewa irin wannan dabi’a “na nuni da karancin kima ga tsarin dimokuradiyya,” yana kiran a daina “karfafa ’yan siyasa masu yawo daga jam’iyya zuwa jam’iyya.”

Kotun ta kuma umurci Gummi da ya mayar da dukkan albashi da alawus da ya karɓa tun daga 30 ga Oktoba, 2024, lokacin da ya sauya sheka, zuwa ranar yanke hukunci.
Bugu da ƙari, kotun ta ci tarar Naira 500,000 a kan Gummi tare da bayar da kudin ga masu shigar da kara.

Post a Comment

Previous Post Next Post