Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa umarnin kotu da aka bayar bazai hana ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta na ƙasa ba, wanda aka tsara zai gudana nan ba da jimawa ba.
A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar ya fitar, PDP ta ce tana girmama kotu da doka, amma babu wani abu a cikin umarnin da zai iya dakatar da shirin taron, wanda a cewar jam’iyyar, yana da muhimmanci wajen ci gaban dimokuraɗiyya da tsarin mulkinta na cikin gida. “Jam’iyyarmu ta girmama kotu, amma umarnin da aka bayar bai hana mu shirya taronmu na kasa ba. Shirye-shirye sun yi nisa, kuma mambobinmu daga sassa daban-daban na kasar suna da kwarin gwiwar halarta,” in ji jam’iyyar a cikin sanarwar.
PDP ta ƙara da cewa babban taron zai kasance wata dama ta ƙarfafa haɗin kai, sake fasalin tsarin mulki, da tsara sabbin manufofi da za su ƙarfafa jam’iyyar a fagen siyasa, musamman yayin da ake shirin zaɓen shekarar 2027.
Sai dai wasu daga cikin mambobin jam’iyyar sun bayyana damuwarsu cewa wannan lamari na iya jawo rikici a cikin jam’iyya, musamman idan ɓangarorin adawa suka ci gaba da amfani da kotu wajen yin tasiri kan yadda za a gudanar da taron.
A ƙarshe, PDP ta tabbatar da cewa komai yana tafiya cikin tsari, kuma kwamitin shirya taron yana aiki kafaɗa da kafaɗa da lauyoyin jam’iyyar don tabbatar da cewa dukkan shirye-shirye sun yi daidai da tanadin doka da kundin tsarin jam’iyyar.