Mazauna birnin Garoua na ci gaba da zanga-zangar adawa da mulkin Shugaban Ƙasa Paul Biya, yayin da suke jiran sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
Tuni jami'an tsaro suka tarwatsa wasu masu zanga-zangar da hayaƙi mai sa hawaye a wasu sassan ƙasar.
Babban ɗantakarar adawa Issa Bakary ne ya nemi magoya bayansa su gudanar da zanga-zangar, inda ya zargi gwmanatin Biya da yunƙurin sauya sakamakon zaɓen.
A gobe Litinin ne hukumar zaɓen ƙasar za ta bayyana sakamakon. Amma tuni Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara.
