Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kai samame da sassafe a ranar Lahadi, 26 ga Oktoba, a Proxy Night Club, da ke lamba 7, titin Akin Adesola, Victoria Island, Lagos, inda aka gano ana gudanar da taron shan miyagun ƙwayoyi.
Hukumar ta kama mutum sama da 100, ciki har da mai gidan kulob ɗin kuma mashahurin ɗan Lagos, Mike Eze Nwalie Nwogu, wanda aka fi sani da Pretty Mike.Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya bayyana cewa an kama waɗanda ake zargi tare da kai su ofishin hukumar domin tantancewa, bayan da aka gano akwatunan kwayoyi haramtattu, ciki har da Loud da laughing gas, daga wajen taron da kuma a cikin ɗakin ajiya na kulob ɗin.
Ya ce samamen ya biyo bayan samun bayanan sirri ne kan taron, inda jami’an hukumar da suka shiga wajen a ɓoye tun ƙarfe 11 na dare ranar Asabar, 25 ga Oktoba, suka watse taron da misalin ƙarfe 3 na daren ranar Lahadi, 26 ga Oktoba, bisa ga tsarin aikin hukumar (SOPs).
A wani samamen daban, NDLEA ta gano hodar iblis (cocaine) da ake shirin fitarwa zuwa Biritaniya, da aka ɓoye cikin kwalayen cream, da kuma methamphetamine a cikin na’urar dumama ruwa (water heater).
An gano faifan hodar iblis guda 70, masu nauyin kilo 3.60, da aka ɓoye cikin kwalayen cocoa butter formula body cream da ake shirin tura wa London, United Kingdom, a export shed na filin jirgin sama na Murtala Muhammed International Airport (MMIA) Ikeja, Lagos. An kama mutane uku bayan bincike da ya ɗauki makonni biyu.
An kama Lawal Mustapha Olakunle, ɗan kamfanin sufuri da ya kawo kayan, sannan daga baya aka cafke Ogunmuyide Taiwo Deborah, wata ma’aikaciyar lafiya, da kuma Mutiu Adebayo Adebiyi, shugaban kamfanin tafiye-tafiye na Mutiu Adebiyi & Co., a ofishinsa da ke 23 Ladoke Akintola Street, Ikeja GRA, ranar Litinin, 20 ga Oktoba.
A wani lamarin makamanci, jami’an NDLEA a Akanu Ibiam International Airport (AIIA) Enugu, sun kama wani ɗan ƙasar Lesotho mai shekaru 35, Lemena Mark, wanda ke ƙoƙarin fitar da gram 103.59 na methamphetamine da aka ɓoye a cikin diabeta herbs coffee tea pack, zuwa ƙasar Philippines, ta jirgin Ethiopian Airlines, ranar Laraba, 22 ga Oktoba.
Haka kuma, hukumar ta kama Umar Abubakar, mai shekaru 40, a Bode Saadu, ƙaramar hukumar Moro, Jihar Kwara, bayan gano kapsul 21,950 na tramadol 250mg da aka ɓoye cikin na’urar dumama ruwa mai Lita 100, ranar Talata, 21 ga Oktoba.