A ƙasar Indiya, an kama kuma an gurfanar da wasu matasa Musulmai bayan sun yi amfani da kalmar “I love Muhammad” a kafafen sada zumunta da kuma a wasu taruka na addini. Wannan mataki ya haifar da cece-kuce sosai tsakanin al’ummar Musulmi da ma sauran ‘yan ƙasa.
Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an tsaro sun cafke matasan ne bisa zargin cewa kalamansu na iya haifar da tashin hankali ko rarrabuwar kawuna a tsakanin al’umma. Sai dai Musulman ƙasar sun yi tir da wannan aiki, suna masu cewa gwamnati tana cutar da Musulmai ne saboda imanin su.
Wani malamin addini daga jihar Uttar Pradesh ya ce: “Ba laifi ba ne mutum ya nuna soyayyarsa ga Annabi Muhammad (SAW). Wannan matakin gwamnati yana nuna yadda ake danne ‘yancin Musulmai a ƙasar.”
A cewar kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam, irin wannan kama da gurfanarwa na ƙara haifar da tsoro a tsakanin Musulmai, inda wasu ke ganin kamar ana ƙoƙarin hana su bayyana imani da addininsu a fili.
Tun bayan hawar gwamnatin Hindu ta Jam’iyyar BJP a ƙarƙashin Narendra Modi, an sha samun rahotannin nuna wariyar addini da hare-hare kan Musulmai a sassan ƙasar.
Musulman ƙasar na kira ga duniya da ta tsoma baki, domin kare haƙƙinsu da tabbatar da adalci ga duk wanda aka kama saboda soyayya ga Annabi Muhammad (SAW).