Kamar yadda ake gani a wasu shafukan sada zumunta da sauran kafofin watsa labarai, Saudiyya na shirin gina katafaren filin wasa na sama wanda shi ne na farko a duniya, wanda ake kira "NEOM Stadium", kuma ana ƙoƙarin haɗa shi ne da birnin "The Line" na zamani wanda Saudiyya ke shirin yi. Za a gina wannan fili mai tsawo da faɗi sama da ƙasa, da ke da tsayin mita 350, daidai da tako (1,150 na ƙafafu).
Filin wasan, wanda zai ƙunshi kujeru 46,000, zai yi amfani da makamashi mai sabuntawa. An shirya buɗe filin wasan ne a shekara ta 2032, kuma zai ɗauki nauyin wasanni, har zuwa wasan daf da na kusa da ƙarshe (Quater Finalal) a gasar cin kofin duniya ta FIFA ta 2034.
Wannan wani yunƙuri ne na kafa sabon ma'auni a fannin aikin Injiniyoyi musamman ta fannin gine-gine, kuma duniya a shirye take.
