Yaro Ya Fashe Idanun Kanwarsa a Yunkurin Yin Asiri A Bauchi

Wani yaro mai suna Auwalu Muhammad ya cire idanun ƙanwarsa, Rukayya Muhammad mai shekaru bakwai, a yunƙurin yin asiri don samun dukiya a ƙauyen Wailo, ƙaramar hukumar Ganjuwa, Jihar Bauchi.

Rahotanni sun ce Auwalu ya ja ƙanwarsa zuwa daji inda ya kai mata hari da niyyar kashe ta. An garzaya da ita Asibitin Koyarwa na ATBUTH Bauchi, inda likitoci suka tabbatar cewa ta rasa ganin duniya har abada.

Kakakin ’yan sanda na jihar, CSP Ahmed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kama Auwalu tare da wasu mutum shida da ake zargi da hannu a cikin aika-aikar.

Kwamishinan ’yan sanda, CP Sani-Omolori Aliyu, ya umurci a miƙa shari’ar ga SCID domin cikakken bincike, tare da alkawarin hukunta duk masu hannu a wannan mummunan aiki.

Post a Comment

Previous Post Next Post