Kwamitin shirya Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya, 2025, yana son sanar da jama’a, musamman marubuta da malamai da ɗalibai da masu sha’awar adabin Hausa, cewa, za a tsayar da rijistar mahalarta taron saboda an riga an kai adadin mutanen da ake buƙata domin gudanar da taron cikin tsari da aminci.
An tsayar da ranar Alhamis, 23 ga
Oktoba, 2025 a matsayin rana ta ƙarshe ta kammala rijista.
Daga wannan rana, babu wanda zai ƙara
iya yin rajista ko canza bayanan rijista da aka riga aka kammala.
Wannan mataki na tsayar da
rijista ya zama dole ne saboda kwamitin ya fara shirin samar da ingantattun
abubuwan more rayuwa da jin daɗin
mahalarta taron, domin tabbatar da cewa taron zai gudana bisa tsarin da ake
gudanar da taruka na ƙasa da ƙasa.
Kwamitin shirye-shiryen taron
ya tanadi:
Wurin kwana mai inganci ga dukkan
mahalarta da suka yi rijista a kan lokaci,
Abinci da sha mai kyau da tsabta,
Da kuma tsarin taro na zamani da
zai bai wa kowa damar koyo da musayar ra’ayi da hulɗa da ƙwararru daga sassa daban-daban na duniya.
Taron Ranar Marubuta Hausa na
Duniya, 2025, wanda za a gudanar a Jihar Jigawa, na da nufin ɗaga martabar harshen Hausa
da marubuta, tare da haɗa
su da sabbin fasahohi da dabarun da ake amfani da su a duniya wajen rubutu,
fassara, da ilimin harshe.
Kwamitin yana yaba wa duk wanda
ya nuna sha’awa ko ya riga ya yi rijista, tare da neman afuwar wadanda ba su
samu damar kammala rijista ba.
Wanda ke sha'awar zuwa taron ba
yi rijista ba zai iya halarta, amma ba za a bashi masauki ba da kayan da suka
shafi taro.
Za a ci gaba da sanar da bayanai
masu muhimmanci ta kafafen sada zumunta da shafin taron.
Dr. Abdulrahman Aliyu
Sakataren Kwamitin Shirya
Taron Ranar Marubuta Hausa ta Duniya, 2025
