An samu kaurewar rikici tsakanin mahaifin wata ɗaliba da kuma wani Malami a Jami'ar Maryam Abacha American University sakamkon yadda mahaifin ya zagi malamin kan hukunta ɗalibar da ya yi kan wani laifi da ta aikata duk da cewa ba a bayyana abin da ɗalibar ta yi ba.
Mahaifin ya yi tattaki ne zuwa makarantar tare da bin malamin har ɗakin jarabawa ya ci mutuncinsa, ita kuma ta kira mahaifin ya zo har cikin ɗakin ya ci mutuncinsa. An jiyo ɗalibar a wani gajeren bidiyo na rikicin wanda ke yawo a kafafen sada zumunta na faɗa wa Malamin cewa "ba fa kyauta mu ke zuwa karatu a makarantar nan ba fa, kuɗi mu ke biya amma kuma a rinƙa wulaƙantamu kullum sai an bamu wahala? Haba!".
Wannan furuci da ta yi ya fusata mutane da dama da su ka kalli bidiyon musamman Malaman makaranta la'akari da yadda ake yawan samun ɗalibai da ke da irin wannan tunani musamman a makarantun kuɗi irin haka.
Yayin da masana su ka bayyana abin da mahaifin yarinyar ya yi na zuwa har ɗakin jarabawar jami'ar wadda ke Kano ya ci mutuncin malamin a matsayin taka dokar hukumar NUC, an buƙa mahukuntar jami'ar da su ɗauki tsatsauran mataki a kan yarinyar da kuma mahaifin domin kare martabar jami'ar da kuma ma'aikatanta.
Ku mene ne ra'ayinku a kan wannan lamari?