Cole Palmer ya samu mummunar raunin da zai hana shi taka leda na tsawon mako shida.
Palmer ɗan ƙwallon Ingila wanda yake taka leda a ƙungiyar Chelsea da ke buga gasar Premier League, ba zai samu buga wasannin da ƙungiyar za ta buga ba har sai wasannin watan Disamba.
Dan wasan ba zai taka leda a wasanni 11 da kungiyar za ta buga ba na gasar cin kofin Premier da Champion da kuma EFL Cup.