Zelenskyy na neman tattauna batun yaƙin Ukraine da batutuwan tsaro.
Rahotanni daga Washington sun bayyana cewa Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, zai gana da Shugaban Amurka Donald Trump a gobe, bayan da Trump ya amince da yin tattaunawa kai tsaye da shugaban Rasha, Vladimir Putin.
A cewar jami’an diflomasiyya, wannan ganawar tana da matuƙar muhimmanci domin Zelenskyy zai yi ƙoƙarin nema tallafi da fahimtar matsayar Amurka kan rikicin da ke tsakanin Ukraine da Rasha. Ana sa ran za su tattauna batutuwan tsaro, taimakon soji, da hanyoyin kawo ƙarshen rikicin.
Wannan na zuwa ne a wani lokaci da ake ganin Amurka tana ƙoƙarin daidaita dangantaka da Rasha, abin da wasu ke ganin na iya shafar goyon bayan da Ukraine ke samu daga Amurka. Sai dai fadar White House ta bayyana cewa ganawar ba za ta rage goyon bayan Amurka ga Ukraine ba, illa dai don taimakawa wajen samar da mafita mai dorewa ga rikicin.