Yadda Aka Kashe Osama Bin Laden da Kuma Inda Aka Binne Shi

 ranar 1 ga watan Mayun 2011, da kimanin ƙarfe 11:30 na dare ne shugaban Amurka na wancan lokaci Barrack Obama ya sanar da kisan Osama Bin Laden. An kashe Bin Laden ne a wani gida da ke birnin Abbottabad na ƙasar Pakistan bayan dogon lokaci na tattarawa da sarrafa bayanan sirri.

Osama Bin Laden

Gidan da aka kashe shugaban na AlQaeda ya kasance yana da tsaron da ba a saba gani ba, Katanga mai tsayi da wayar tsaro, tagogi marasa haske, da kuma rashin intanet da sabis ɗin waya. Ana ƙona duk wata sharar da aka samu a cikin gidan. Girma da kuma tsarin gidan ya bai wa hukumomin Amurka mamaki. Gidan na zagaye ne da wata katanga mai tsawon mita huɗu zuwa shida, kuma gidan ya nunka gidajen da ke makwaftaka da shi wajen girma sau takwas, sai dai babu tarho kuma babu intanet.

Wani abu da aka lura da shi shi ne mazauna gidan ba su da wani aikin yi ko kuma hanyar samun kuɗin da zai sa su mallaki ƙaton gida kamar wannan. Hakan na ɗaya daga cikin abubuwan da suka ƙara janyo hankalin jami'ai a kan gidan. To amma wani abu shi ne Osama bai taɓa fita daga gidan ba, saboda haka dole ne Amurkawan su san dabarar da za su gano wanda ke cikin gidan.

Yayin da suke bincike da sanya ido kan gidan, sai suka lura da wani mutum yana safa da marwa a lambun gidan, inda suka yi zargin Osama bin Laden ne.Daga nan sai suka auna girmar inuwarsa. Jami'an sun kira wani ɗan jarida mai suna John Miller, wanda ya taɓa yin hira da Osama a shekarun 1990, inda suka buƙace shi da ya ba su bidiyoyin da ya ɗauka na Osama yana tafiya domin kwatantawa da hotunan da suke da su na mutumin da suka gani yana zirga-zirga a gidan. Sai suka lura kamanceceniyar ta yi yawa. Ba kawai inuwar ba, har ma da ɗan ɗingishin da Osama yake yi ya zo daidai da abin da aka gani a bidiyon.

Haka nan wani abu da ya haifar da zargi shi ne yawan kayan da aka shanya a saman gidan, wanda ke nuna cewa akwai mutane da yawa da ke rayuwa a gidan. Daga nan ne a ranar Lahadi, ƙwararrun dakarun Amurka daga rundunar Navy Seal Team Six ta ƙaddamar da samame a gidan a birnin Abbottabad, mai nisan kilomita 100 daga birnin Islamabad.

Shugaba Obama ya ce "babu wani ba'amurke da aka cutar a lokacin samamen." Wani jami'in Amurka da ya yi ƙarin haske kan harin ya ce sojojin sun kwashe kimanin minti 40 lokacin samamen. Haka nan wani babban jami'in na Amurka ya ce ba tsegunta wa kowace ƙasa bayanan sirrin da aka tattara ba gabanin samamen, ciki kuwa har da ƙasar Pakistan.

"Mutane ƙalilan ne daga cikin gwamnatinmu suka san da samamen kafin a ƙaddamar da shi," in ji jami'in.

Shugaba Obama ya sanar cewa dakarun Amurka sun samu nasarar ɗaukar gawar Osama ne bayan "musayar wuta". Inda daga bisani gwajin halittar gado ya tabbatar da cewa lallai Osama ne aka kashe. Jami'an ma'aikatar tsaro ta Pentagon sun ce an binne Osama ne a teku ne bayan yi masa sallah a kan wani jirgin ɗaukar jiragen yaƙi na Amurka.

Dalilin yin hakan, kamar yadda shugaban hukumar tattara bayanan sirri na Amurka a wancan lokaci Leon Panetta ya bayyana shi ne domin kada a binne shi a doron ƙasa, kabarinsa ya zama tamkar wajen bauta.

Post a Comment

Previous Post Next Post